Kamfanin Instagram Ya Kara Wasu Alamu Na Bayyana Ra'ayoyi A Shafinsa

Nan bada dadewa ba dandalin sada zumunci na Instagram zai koma kamar na uwar dakinsa Facebook, ta yadda mutane zasu iya nuna so da tsokaci da wani ya rubuta.

Kamfanin Instagram ne ya fitar da wannan sanarwar cewa zai baiwa mutane damar yin tsokacin da duk wasu sharhi ko tsokacin da mutane suka rubuta, kamar yadda akeyi a shafin Facebook.

Haka kuma mutane zasu iya nuna jin dadinsu ga abin da aka rubuta ta hanyar amfani da wata karamar alamar zuciya mai jar kala, maimakon wadda ake amfani da ita wajen nuna kaunar hotuna a shafin.

Dalilan da kamfanin ya bayar na kara alamun zuciya a shafin shine domin ya banbanta alamar jinjinawa da ake amfani da ita a shafin Facebook. Kamfanin yace yana kokari ganin ya kirkiro abubuwan da zasu kayatar da masu amfani da dandalin.

A wani rubutu da ya kafe a yanar gizo, shugaban Instagram Kevin Systrom, yace baya ga hotunan zuciya da aka ‘kara, kamfanin ya ‘kara wasu hanyoyi biyu domin tabbatar da kwanciyar hankalin masu amfani da dandalin. Na farko shine mutane zasu iya rufe duk wani tsokaci da akayi wanda basa so, na biyu mutane zasu iya rufe duk wani mutum da basa so dake bibiyar shafinsu ba tare da ya sani ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Kamfanin Instagram Ya Kara Wasu Alamu Na Bayana Ra'ayoyi A Shafinsa