Babban yunkurin Kamaluddeen, a rayuwa shine yaga cewar matasa a Najeriya, sun kai duk wani mataki da matasa, suka kai musamman irin na matasan kasar Ingila, da ya gani ma idon shi, duk da cewar matasa a gida Najeriya, suke da kason baya a wajen harka cigaba ta tallafi daga gwamnatoci da kamfanoni.
Cigaban kasa ya rataya akan matasa, dole ne matasa su tashi tsaye, don ganin sun taimaka wajen cigaban kasa, a kowane hali. A cewar shi “Bamu da wata kasa da ta wuce Najeriya, dole mutashi don ci gabanta. Shi kuma cigaba sai da ilmi yake samuwa, saboda haka matasa mu tashi tsaye mu nemi ilimi don cigaban kanmu da Nijeriya”.
Sai ya kara da cewar babu girma a wajen neman ilimi, duk wanda ya sama kanshi kirman kai, to babu shakka zai zaman a baya a cikin sahun abokan shi. Don haka dole ne ga matasa su tashi tsaye wajen neman ilimin zamantakewa a kowane irin hali suke. Iri-iren bincike da ake gudanarwa a duniya, yanzu mafi akasarin su matasa ke yi, don haka matasa a Najeriya, ya kamata su cigaba da shiga ko ina don a dama da su.
Idan Allah yasa Kamaluddeen, ya kammala karatun shi na digirin digirgir, yana fatar ya koma Najeriya, da zummar cigaba da aikin da suka fara shekaru da suka gabata, a wajen kara jawo hankalin matasa, da su tashi tsaye. Kana yana ganin cewar duk wani matashi dake karatu, kada ya dauka cewar ta hanyar karatun ne kawai zaiyi arziki.