Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Face Book: Yanzu Matasa Zasu Iya Buga Wasan Game A Manhajar Sakon Gaggawa!


Sabon Tsarin Wasan Game Na Facebook
Sabon Tsarin Wasan Game Na Facebook

Kamfanin zumunta na facebook, ya kaddamar da wata sabuwar hanya, da mutane kan iya kashe lokaci mai tsawo a shafin sakon gaggawa. Daga yanzu mutane zasu iya amfani da manhajar aika sakon gaggawa “Messenger App” don buga shahararrun wasannin game. Wannan wata hanyar kayatar da shafin zumuntar ne ga ma’abota sha’awar wasan game.

Sabon tsarin wasan game din, dai anfara amfani da shi ne a kasashe talatin 30, a fadin duniya, wanda zasu iya buga wasanni goma sha bakwai 17, wadanda suka hada da su "Pac-Man, Space Invaders" duk wanda ke amfani da waya mai dauke da manhajar iOS da Android, tsarin operating system, zasu iya buga wasan a kowane lokaci.

Mutane kan iya buga wasan game koda kuwa, suna tsakiyar magana da mutane a kan wayar su, wanda matasa zasu iya kalubalantar abokan su a wajen kwarewa da wasan game din.

Tun bayan kirkirar tsarin sakon gaggawa, mai cin gashin kanshi da kamfanin facebook, suka kirkira a shekarar 2014, mutane sun rungumi tsarin don ganawa da sauran dangi a ko ina a fadin duniya.

Yanzu haka an kara kayatar da tsarin, inda mutane zasu iya amfani da shi wajen biyan kudi, dangane da wata siyayya da su kayi, a fadin duniya. Kimanin mutane sama da billiyan daya ne ke amfani da wanna tsarin, na aika sakon gaggawa na facebook, inda ya zama na farko a cikin jerin uku da ake dasu a fadin duniya. Daga facebook sai tsarin Whatsapp, da kamfanin ya siya a shekarar 2014.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG