Maddie Coleman, matashi dauke da labari mai ban’al’ajabi. Tun ina ‘yar shekaru goma sha hudu 14. Likitoci suka ga yamun cewar, gaskiya abune mai wuya idan zan iya haihuwa, a iya tsawon rayuwa ta. Domin kuwa an haife ni dauke da wata irin cuta mai suna “Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser” a turance.
Ita dai cutar, takan hana mata samun juna biyu, duk mace dake dauke da wannan cutar, bata samun iya haihuwa. A dai-dai lokacin da likitoci suka gayamun hakan, sai mahaifiya ta cikin tausayi ta dauki akawalin cewar, zata haifar mun 'ya'ya, idan lokacin yayi.
A wannan shekarar bayan Maddie, tayi aure kuma tana da masaniyar cewar ba zata iya haihuwa ba, sai ta gayama mijin ta Mr. Tyler, cewar mahaifiyar ta, tayi alkawalin zata daukar mata ciki na tsawon watanni tara 9.
Megan Barker, mai shekaru arba’in da takwas 48, itace mahaifiyar Maddie, tace lokacin cika alkawali yayi, don haka likitoci sun dauki kwayoyin hallitun haihuwa goma sha biyu 12, na ‘yar ta da na mijin ta, wanda aka saka cikin mahaifar, mahaifiyar yarinyar.
Wata daya, bayan saka kwayayen hallitun dan’adam da akayi a cikin mahaifar, Maddie, sai likitoci suka tabbatar da cewar, tana dauke da ciki. Bayan wata tara mahaifiyar Maddie, ta haifi jariri, inda ‘yan uwa da abokan arziki, sama da mutane goma sha uku 13, suka taru a cikin dakin haihuwar, don taron d'a ko jika.
Don haka mahaifiyar yarinyar, ta cika alkawalin ta, na daukar ciki da haifarwa ga ‘yar ta. Maddie ta bayyana ma jaridar “InsideEdition” cewar mahaifiyar ta, ta cika alkawali. Kuma tana daukar nauyin yaron kamar yadda kaka ke yima jika.