Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taswirar Zanen Hannun Mutun Na Bada Kariya Wajen Satar Waya!


Zanen Yatsan Hannu
Zanen Yatsan Hannu

Wani cigaba kan iya zama mafita ga rayuwar yau da kullun. Musamman idan akayi la’akari da yadda cigaban zamani yake kara bama mutane dama, wajen amfani da zanen hannu don kulle waya ko kwanfuta, a matakin kara samar da tsaro.

Sau da dama mutane kanyi amfani da yatsan su, wajen kulle waya, ba sai sunyi amfani da lambobi da akanyi amfani da su wajen kulle wayoyin hannu ba. A wasu lokkuta hakan yakan iya zama mafita, a wasu lokkuta kuma su kan iya zama matsala ga sirrin mutane.

A yunkurin sun a magance matsalar amfani da lambobin sirri, kamfanin Apple, Microsoft, da wasu kamfanonin kimmiya, na shawartar mutane da su kokarta, wajen amfani da zanen hannun su, wajen kulle wayoyin su da kwamfutoci, don kara karfin tsaro mai inganci. Suna kara kaimi wajen samar da wata kafar amfani da kwayar ido don bude waya, a cikin yunkurin samar da tsaro mai nagarta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG