Sakamakon Firimiya Lig 2016/2017 Mako Na Goma Sha Uku

Asabar da ta gabata 26/112016 an fafata wasanni na firimiya lig na kasar Ingila 2016/2017 sati na sha uku

Kungiyar kwallon kafa ta Burnley ta sha kashi a hanun Manchester City daci 2-1

Liverpool ta doke Sunderland da kwallaye 2-0

Swansea ta lallasa Crystal Palace daci 5-4

Leicester City tayi canjaras 2-2 da MiddleBrough

Hull City tayi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Westbromwich

Chelsea nada 2 Tottenham nada 1.

A Ranar Lahadi kuwa kungiyar Watford ta sha kashi a gidanta daci 1-0 a hannun Stoke City

Arsenal ta samu nasarar doke AFC Bournemouth daci 3-1

Manchester United ta yi kunnen doki 1-1 tsakaninta da Westham

Southampton tasha Everton 1-0.

Asaman Teburin firimiya lig kuwa har yanzu Chelsea ke kan gaba da maki 31

Liverpool na matsayi ta biyu da maki 30

Manchester City na mataki na uku itama da maki 30

Yayinda a kasan tebur Hull City tana matsayi ta gomasha takwas da maki 11

Swansea na matsayi ta gomasha tara da maki 9

Ita kuwa Sunderland tana mataki na Ashirin ne da maki 8.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakamakon Firimiya Lig 2016/2017 Mako Na Goma Sha Uku