Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta yiwa Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta Najeriya, watau Super Falcons, alkawarin cewa zasu samu kudadensu na alwus alwus nan bada jimawa ba.
Wanna ya biyo bayan abinda hukumar ta wasan kwallon kafar Najeriya, ta ji cewa ‘yan kungiyar a shirye suke dasu kauracewa wasan su na karshe da Kenya a rukuninsu, koda yake sun dai doke Kenya da ci 4 da babu.
Shugaban kwamitin fasahu na hukumar ta NFF, Chris Green, ne ya bayyanawa ‘yan wasan wannan albishir din ta wayar talho, ya kara da cewa “mako mai zuwa idan kuka ganin a kasar Kamaru, to tabbaci hakika nazo da kudaden ku”.
Hukumar dai tace zata tabbatar da cewa an biyasu kudadensu kafin ranar da zasu buga wasan su na kusa da na karshe da kasar Afirka ta kudu.
A na sa ran cewa ‘yan kungiyar zasu sami dala dubu hudu ladar lashe wasa da dubu biyu ladar yin kunnen doki dama sauran alwus alwus din da yakamata a biyasu.