Messi Da Neymar Zasu Fafata Wajan Samun Lambar ( Fifa Puskas Award 2016)

Hukumar dake kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa guda goma wadanda zasu fafata wajan gasar cin lambar yabo ( Fifa Puskas Award 2016)
Wannan lambar yabon ana bada ita ne ga 'yanwasan kwallon kafa daga bangaren maza da mata ga duk wanda yasha kwallon da tafi kowacce kwallo kyau a shekarar inda akan fara daga watan Oktoba zuwa watan Oktobar wata shekara.

An fara wannan bada wannan kyautarne a shekara ta 2009 karkashin jagorancin Tsohon shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter, an kuma samu wannan suna Puskas ne daga wani tsohon dan wasan Real Madrid, mai suna Ferenc Puskas, dan kasar Hungry, wanda ya yi wasa tun karni na ashirin (20 century) inda ya zurara kwallaye har guda 512 a wasanni 528 da ya buga.

Puskas ya yi tashe kwarai a yayin da yake fagen wasa, kuma an haifeshi a shekarar 1927, ya rasu a shekara ta 2006, lokacin yana da shekaru 79, da haihuwa a duniya

A cikin jerin Sunayen 'yan wasan da aka fitar akwai Lionel Messi, na Kungiyar Barcelona, wanda ya jefa wata kwallo da ta burge a wasan da kasarsa Argentina, ta fafata da USA, a gasar copa America 2016.

Sai takwaransa Neymar, wanda ya sha Kungiyar kwallon kafa ta Villarreal, a kakar wasa da ta gabata

Sauran Sunayen sun hada da dan wasan Atletico, Saul Niguez, a wasan Atletico, da Bayern Munich, sai kuma dan wasan kasar Wales, Robson Kanu a wasansu da kasar Belgium, Eufa 2016.

Daniuska Rodriguez, yar kasar Venezuela, da ta sha a wasan Venezuela da Colombia (U17 women 2016).

Simon Skrabb, a wasan Gefle da Atvidaberg 2015. Moh'd Fai'z, na Malaysia, a wasan Penang da Pahang 2016. Akwai kuma Mario Gaspar, a wasan Spain da England 2015.
Hlompho kekana, na South Africa, a wasansu da Cameroon 2016.
Marlone, na Brazil a wasan Corinthians da Cobresal 2016.

Your browser doesn’t support HTML5

Messi Da Neymar Zasu Fafata Wajan Samun Lambar ( Fifa Puskas Award 2016)