Sabuwar Taswirar Birnin Abu Dhabi, Zata Haskaka Duniya!

Taswirar Birnin Abu Dhabi

Hukumomin gwamnatin kasar Dubai, da ke daular kasashen larabawa. Sun rattaba hannu akan wata sabuwar kwantiraki da wani shakararren kamfanin kasar Amurka, don kara fadada babban birnin da sake bude wani kayataccen birni.

Kasar Abu Dhabi, tana kara bunkasa a harkar kasuwanci, shakatawa, yawon bude ido, daga kowane bangare na fadin duniya. An kaddamar da wannan yarjejeniyar ne katafaren babban otel dinnan, da yafi kowane gini tsawo a fadin duniya “Burj Khalifa.”

Babban abun da suke ma burin cimma wa, a wannan tsari na kara kawata babban birnin, shine su kara jawo hankalin mutanen duniya, garin ya zama gari da yafi kowane gari tsari a fadin duniya. Yanzu haka dai birnin dai shine birnin da yafi kowane birni samun cigaba a cikin kankanin lokaci.

A cewar jagoran jarjejeniyar Mr. Rob Lloyd, yana da yakinin cewar wannan birnin idan aka kammala sabon tsarin, zai zama birni da babu wani cigaban kimiyya da fasaha da baza’a iya samu a wajen ba, duk da cewar an dade ana amfani da mota mai tuka kanta a birnin, da duk wani sabon abu na zamani.