A shirinmu na mata yau mun sami bakuncin matashiya me sana’ar hannu me suna Kibonen Nfi, ‘yar kasar Kamaru mai zama a birnin Newyork na kasar Amurka, Kibonen ta shigo kasar Amurka kusan shekaru goma da suka gabata inda taga cewa ya dace ta kama sana’a domin a cewarta, babu maraya sai rago.
Matashiyar me matsakaitan shekaru ta bayyana cewa tana sayo kayayyakin ne daga kasar kamaru sa’annan ta sarrafasu kana ta sayar a nan kasar Amurka, kai harma ta fara samun masu shi’awar kayan nata daga kasar Austarlia.
A tattaunawarsu da ma’aikaciyar sashen Hausa na muryar Amurka, Marya Bugaje, ta fara da cewa;
Sunana Kibonen Nfi, "ni ‘yar asalin kasar Kamaru ce, kuma na kwashe shekaru kusan goma a nan kasar Amurka, sanar’ar hannu ce aiki na, ina sana’ar dinki a kasa ta Kamaru, kuma buri na a rayuwa shine in kara karfafa dangantaka tsakanin al’adu na duniya daban daban ta hanyar amfani da sutura. A kasata kuma babban burina shine in samarwa da matasa maza da mata guraben ayyukan yi".
Da aka tambayeta dalilin da yasa ta fara wannan sana'a sai ta amsa cewa
"Gaskiya tun ban san komi dangane da sana’ar dinke dinke ba nake shi’awar ta, sana’a ce data dade cikin raina, dan haka dana zo kasar Amurka naga yadda sana’ar take sai na fara kokarin gwada fara tawa ta kaina, amma abinda nayi shine dana koma kasata sai na fara kokarin hada kaya irin na gargajiya kama daga sarkoki, abin hannu da kayan sawa, dana shigo da su sai naga jama’a na shi’awarsu sosai har suna saye, hakan sai ya kara min karfin gwiwa".
daga karshe ta yi kira ga matasa maza da mata inda ta ce kowa yayi amfani da irin baiwar da Allah ya bashi, idan mutum ya gano irin baiwarsa, lallai hakan zai sa yayi amfani da ita cikin kwarewa da shi’awa kuma daga karshe mutum ya sami nasara.
Saurari cikakkiyar hirar anan.