Sabon Kudurin Kamfanin Facebook

Kamfanin Facebook ya kudiri aniyar karfafa yawan amfani da hotunan bidiyo a shafinsa, kama daga bidiyon da mutane ke dauka domin nishadi zuwa wasu muhimman abubuwa da ke faruwa a duniya, yanzu mutane zasu kalli hotunan bidiyo a dandalin babu sassauci.

Aniyar Facebook a yanzu itace ganin dandalin ya zamanto guri ne da mutane zasu yawaita kafewa da kallon bidiyo har ma da tallace tallace, a kokarin da kamfanin ke yi na karfafa kasuwancinsa.

Yanzu haka dai da alamun kwalliya zata biya kudin sabulu, kasancewar tuni manyan kamfanonin suka fara gwada wannan sabuwar hanyar da kamfanin ke kokiri ganin ta samu nasara. Missali, cikin wannan shekarar ne kamfanin General Motors ya kaddamar da sabuwar motarsa mai amfani da lantarki ta Chevy Bolt kai tsaye ta Facebook live.

Facebook dai ya samu nasarar rikida zuwa wayoyin hannu baya ga shafunan allon kwamfuta, duk kuwa da kokwanto da akeyi. Yazu kuma Facebook na kokarin sayarwa da masu talla hotan bidiyo, wanda hakan ke nunin yadda kamfanin zai kara samun kudin shiga.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Kudurin Kamfanin Facebook