Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ina Isar Da Sakonnin Zaman Lafiya Da Kauna Ta Waka - Inji Hafizu Inibi Dorayi


Mawaki Hafizu inibi Dorayi, ya ce yana isar da sakonnin zaman lafiya da hadin kai da ma jan hankali ta hanayr rera waka, ya bayyana haka ne a yayin zantawa da wakiliyar dandalinvoa Baraka Basahi

Ya ce ta hanayar waka yake nunawa al’umma cewar waka sana’a ce da ke isar da sakonnin ga masu sauraro, kuma ya kara da cewa babban burinsa a rayuwa shine ya rera waka da zai wayi gari a sanya shi a ciki wani fim.

Ya ce ya gamsu da sana’ar waka duk kuwa da cewar yana da wata sana’a bayan waka, amma ya kara da cewa waka tayi masa komai.

A fannin mu na tsegumi kuwa, fitattacen mawakin nan Iyanya ya ce yana bakin cikin rashin yin aure a lokacin da mahaifiyarsa ke da rai.

Mawakin ya ce fice da daukakar da yayi ta taimaka wajen rashin samun macen da ke sonsa tsakani da Allah, inda ya kara da cewa hakan ya sa shi cikin mayuwacin hali, tare da cewar da ya san hakan zata kasance da shi da tuntuni yayi aurensa, ko ba komai da yana da yaransa

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG