Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya Ta Biya Siasia Bashin Albashin Watanni Biyar

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF ta biya tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samson Siasia albashin da yake bin hukumar na watannin biyar.

A cewar rahotanni daga Glass House, tsohon kocin kungiyar Super Eagles Samson Siasia da tsohon mai bada shawara na hukumar Gernot Rohr, babu sauran bashi tsakaninsu da hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

“haka ne, na sami albashi na, kuma na gode kwarai” Siasia ya bayyanawa mujallar Goal.

A watan satumba ne Siasia y aba hukumar kwallon kafa ta Najeriya wa’adin sati biyu su biya shi hakinsa ko kuma ya hargitsa shirye shiryen kungiyar Super Eagles na zuwa gasar cin kofin duniya na shekarar 2018.

A lokacin ya bayyanawa kafar yada labarai ta BBC cewa “ na basu sati biyu su biya ni hakki na ko kuma inyi zaman dirshan a ofishin hukumar kwallon kafa ta Najeriya har sai an biya ni.”

Ya kara da cewa “kungiyar kwallon kafa ta kasa na shiye shiyen zuwa wasannin shiga gasar cin kofin duniya a yanzu, ina kyautata zaton abu na karshe da baza sub a shine in daukar masu hankali ba akan abin da suka sa gaba yanzu.”

“Na jaddada masu karara a wasika ta cewar su gaggauta biya na, ni da mataimakina duk hakkin da nake bin hukumar domin bai kamata a rike mani hakki na ba”

Ya kara da cewa “kin biya na hakki na da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi a matsayi nan a jagora wanda ya sadaukar da kansa domin kasa cin mutumci ne da kuma mugunta”

Siasia ne ya jagoranci kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya a shekarar 2016, a wasannin Olympics, na Rio, a kasar Brazil