Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Zasu Sha Mamaki Idan Ba'a Biyamu Ba


Kwallon mata
Kwallon mata

‘Yan kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya, watau Super Falcons, watakila ba zasu sami zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na mata na Afirka ba wanda za’a buga a kasar kamaru.

‘Yan wasan basu ji dadi ba sabili da rashin biyan su kudaden alawus alawus dinsu na baya wanda yakamata a biyasu bayan da suka yi nasaran doke Senegal.

Sunce kawo yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, Naira dubu goma kachal ta baiwa kowace daya daga cikinsu a matsayin kudin mota daga Abuja, zuwa garuruwansu bayan nasarar da sukayi a watan Afirilu.

Sun kara da cewa kasar zata sha mamaki sai idan har hukumar ta biya alawus dinsu na baya da ba’a biya su ba.

‘Yan kungiyar suka ce zasu baiwa mai horar dasu Florence Omagbemi, hadin kai wajan tabbatar da ganin cewa sun kare kambinsu amma da sharadin cewa za’a biyasu alawus alawus dinsu.

Shi dai wannan gasar na cin kofin kwallon kafa na mata na Afirka, za’a fara shine ranar 9, ga watan Nuwamba zuwa 3, ga watan Disamba.

XS
SM
MD
LG