Taron yaye dalibai da aka gabatar a karshen makon da ya gabata, a jami’ar “Ilori” ya dauke hankalin duk mahalarta taron. Domin kuwa, daya daga cikin daliban da suka kammala karatun digirin farko, a fanin aikin likitanci “Dr. Faidat O. Yusuf”
Matashiyar mai shekaru ashirin 20, ta lashe kyaututuka goma sha tara 19, ta zama dalibar da tafi kowane dalibi a cikin dalibai sama da dubu uku da aka yaye. Faidat, ta lashe kyaututuka daga tsangayoyi tara, wanda ba'a taba samun dalibi ko daliba da ya lashe duk kyaututukan a lokaci daya ba.
A zantawa da manema labarai da Faidat, tayi, tace “babu wata mace da bazata iya lashe fiye da abun da ta samu ba, domin kuwa wannan ba wani abu bane illa yadda ta maida hankali wajen karatu da naciya”
Tana da yakin nin cewar, matasa a wannan zamanin sun fi samun duk wata dama da ta kamata, ace matashi ya samu don samun nasara a karatun su. Idan akayi la’akari da yadda suke iya amfani da yanar giwo, wajen bincike a dakukunnan karatu a fadin duniya "Libraries".
Tana ganin yazun matasa basu da, dalilin faduwa jarabawa, ko kuma rashin amfani da damar wannan zamanin, don inganta rayuwar su a nan gaba. Tana kara gode ma iyayen ta, da malaman ta, don irin gudun mawar da suka bata, bata misaltuwa. A karshe ta kalubalanci duk wani matashi ko matashiya, da su tashi tsaye, wajen ganin sun samu ilimi a wannan zamanin.