Kusan kasashe dari biyu 200, ne su ka gabatar da yar jejeniyar rage sinadaran da ke haifar da gurbatar yanayi na iskar “Greenhouse” wanda ake amfani dashi a na’urar sanyaya daki da akafi sani “AC” kana da na firij, a yunkurin yakin rage gurbatar yanayi.
An gabatar da wannan taron na yar jejeniyar rage iskar “Hydrofluorocarbons” A wata ganawa da akayi, a birnin Kigali da ke kasar Rwanda, Inda shugabannin kasashen Afrika suka hallara, suka gano cewar sinadarin dake shiga cikin iskar da mutane kan shaka ta “Carbondioxide” nada matukar illa sosai ga rayuwar dan’adam musamman idan yana yawo a cikin sararrin samaniya.
A wata sanarwa da shugaban kasar Amurka Barak Obama, ya bayar yayi kira ga kasashe dari da casa’in da bakwai 197, da suka gano yanda za’a magance wannan matsalar.
Yace dole su tashi tsaye, su san yanda zasu taimaka ma sauran kasashe suyi, don su magance wannan matsala da ta addabi kowa. Yace dole ne su samo hanyar da za’a magance wannan matsalar, saboda taimaka ma sauran kasashe ta yanda za’a inganta rayuwar su.
Sakataren harkokin kasashen waje na kasar Amurka, John Kerry, wanda ya halarci taron a babban birnin Kigali yace wannan ba karamin cigaba bane. Ya kuma kara da kiran matasa da su maida hankali wajen kirkiro wasu hanyoyi da za’a dinga amfani da na’urorin zamani batare da gurbata yanayi ba.