Bayan da gwamnatin kasar Bangladesh ta fito filli da tayin baiwa duk wani dan yakin sa kai daya tuba tukucin kudi, hukumomi sunce wakilai guda biyu na wata mumunar kungiyar yan ta’ada, sun bada kai.
WASHINGTON, DC —
Daya daga cikin wadanda suka tuban mai suna Abdul Hakim, yace hanyar da suka bi ba mai kyau bace. Abdul Hakim dan shekara ashirin da biyu da haihuwa yace sun lura da kuskuren da suka yi. A saboda haka yace duk kuma wanda ya kama hanyar ta’adanci to yayi tunani domin ba abune mai kyau ba.
Abdul Hakim da Mamudu Hasan suna daga cikin mutane farko da aka baiwa tukuicin kudi, karkashin dabarar karfafawa masu zazafan ra’ayin gwiwa da su ajiye makamansu.. An baiwa kowane mutum tukuicin Taka dubu dari biyar na takardun kudin kasar kimamin dala dubu shidda da dari uku da hamsin ke nan.