Cin Moriyar Guraben Karatu A Rayuwa - Inji Khadija Salisu Umar

Khadija Salisu Umar wata daliba a jam'ar Bayero ta Kano , wacce ta ke karantar harshen Hausa ta ce ta shafe shekaru uku ta na neman gurbin karatu amma abin ya ci tura.

Ta kara da cewa babban burinta a rayuwa shine ta zama lauya, kuma ta nemi gurbin karatun lauya har na tsawon shekaru uku, amma hakan bai yiwuwa ba, daga bisani ta sami harshen Hausa a maimakon abinda ranta ke bukata.

Amma a cewarta gudun kada ta bata lokacinta sai ta amince ta karanta harshen Hausa, kuma tana fatan samun aikin muryar Amurka da zarar ta kamalla karatunta.

Ta ce tana da burin aiki a muryar Amurka bayan wani malaminsu ya bata sharawa tare da bata karfin gwiwa ne ta fara son abinda ta ke karantawa, kuma ta yi kira ga dukkan matasa musamman mata da su yi amfani da duk irin damar da suka samu ta kara karatu domin ilimi baya kwantai.

Khadija ta ce babban abin da ke ci mata tuwo a kwarya bai wuce yadda take gwagwarmaya da koyon harshen Hausa ba duk kuwa da cewa ita bahaushiya ce, ta ce tana samun goyon baya daga wurin abokan karatunta da zarar wani abu ya shige mata duhu.

Saurari cikakkiyar hirar a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Cin Moriyar Guraben Karatu A Rayuwa - Inji Khadija Salisu Umar