Shahararren kamfanin zumunta na Facebook, sun kaddamar da wata sabuwar hanya a shafin zumuntar su, wanda mutane zasu iya amfani da shi wajen siye da siyarwa. Duk wanda yake da wata haja zai iya amfani da damar da suka kira “Marketplace” kasuwar sararri a takaice.
Wannan wata damace da mutane zasu iya amfani da shafin na facebook, wajen tallata hajojin su kodai abun da suka kirkira, kamar wata sana’a, da sukeyi, dinkin hula, sakar kayan sanyi, yin takalma, da dai duk wani abu da mutane kanyi.
Ta haka mutane zasu kuma iya tallata wasu abubuwa da suke da su, kodai sun siya don amfanin su, amma basu da sauran bukata da shi, kamar su mota, mashin, keke, wayar hannu, da duk wani abu da mutun ya keson siyarwa.
Yanzu haka akwai kimanin mutane sama da milliyan darihu da kamfanin suka gano, suna amfani da wannan damar. Duk wanda yake da bukatar amfani da wannan damar, sai yaje saman shafin facebook zai ga wurin dannawa da yayi kama da shago, sai ya shiga, daga nan mutun zai iya ganin hajoji da suke kusa da anguwar su, dama wadanda suke nesa, don kokarin siya ko ciniki.
Idan mutun yaga abun da yake so, sai ya aikama mai kayan sako gaggawa, daga nan sai suyi kokarin fitar da hanyar biyan kudi da karbar kayan.