Maikaba Ya Bayyana Sha'awar Ci Gaba Da Jan Ragamar Kungiyar Wikki Tourist

Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourist dake garin Bauchi Abdullahi maikaba, ya baiyana sha'awarsa ta cigaba da jan ragamar Kungiyar ta wikki a matsayin sa na mai horaswa.

Maikaba ya fadi hakane a wata hira da sukayi da ‘yan jarida bayan kammala wasan da Wikki ta yi tsakaninta da Sunshine a gasar NPFL 2015/2016 wasan karshewanda suka samu nasarar cin sunshine 2-0 ranar lahadi 2/10/2016 a garin Bauchi.

Saidai ya ce kwantiraginsa zai kare ne a karshen kakar wasannin bana amman tunda wannan aikin sana'ar sa ce, ba zai hana wasu kungiya su neme shiba, amman dai yana nan a kan ra'ayinsa na zama a kungiyar inda ya ce duk inda zai je a matsayin sabon wajene sabanin wikki.

Da ake tambayarsa tunda gashi kungiyar sa ta samu nasarar zuwa Confederation cup ko zai sake nemo wasu kwararrun ‘yan wasa da zasu taimaka masa?

Sai yace zai yi amfani da ‘yan wasan da yake dasu a yanzu haka sai dai ‘yan wasu gyare gyare wadanda baza’a rasa ba

Daga karshe yayi godeya wa Allah da ya basu nasarar kasancewa matsayi na uku a gasar Nigeria professional football league ta bana.

Ya kuma gode wa gwamnatin jihar Bauchi bisa namijin korin da tayi wajan samun nasarar, haka kuma Abdullahi Maikaba ya yaba wa jagororin kungiyar Wikki tourist karkashin jagorancin shugabanta Hon Isa Musa Matori tare da ‘yan wasan Wikki da magoya bayanta na cikin gida da na waje tare da illahirin mutanen Bauchi bisa goyan baya da suka bashi a wasannin da wikki tayi na bana.