Masu bincike, sun gano wasu kwayoyin cuta mai suna “Staph” tana bukatar maganin rigakafi, kuma zata iya zama babbar nakasu ga kaji, don kuwa tana iya makalewa a duk inda ake kiwon kaji, don kokarin shiga cikin kaji, wanda daga baya yana iya zama cuta ga duk wani mutun da yaci naman kazar.
Haka kuma ita wannan cutar ta “MRSA” ba kawai a sanadiyar cin naman kaji ake kamuwa da itaba, ana iya kamuwa da ita, a cikin wasu nau’o’in abinci, da kusantar inda mai dauke da cutar yake.
Kamar asibitoci, makarantu, ma’aikatu, kasuwa, da dai duk wurare da mutane kan taru, domin kuwa idan mutun daya na dauke da cutar, zai iya yada ta ga sauran mutane.
A satin da ya gabata hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya, sun gabatar da wani taro, wanda suka kara jawo hankalin mahukunta, da a sanar ma da jama’a haddura da ke tattare, da wannan cuta da kuma hanyoyi da ake bi don kamuwa da ita, mutane suyi hattara.