Mutun Mai Dabi'un Akuya Ya Lashe Lambar Yabo!

Thomas Thwaites Wanda ya Lashe Kyautar Binciken Dabbobi

An gabatar da kyautar jinjinawa ga manya-manyan masana, kuma masu bincike a fadin duniya, an kaddamar da wannan bukin ne, a dakin taro na Sanders a Jami’ar Harvard ta kasar Amurka. Inda aka karrama margayi Ahmed Shafik, na kasar Masar, wanda ya gabatar da bincike akan amfani da wani sinadari, da akanyi amfani da shi wajen kashe bera cikin sauki.

Babban abun da yafi daukar hankali a wajen wannan bukin shine, yadda ka karrama Mr. Thomas Thwaites, shi dai ya gabatar da wani bincike ne, na yadda akuyoyi ke gabatar da rayuwar su.

Don fahimtar ya suke gabatar da rayuwar su, ya koyi yadda dabbobi ke cin ciyayi, kana ya samar da wasu katakai da suka bashi damar yin tafiya kamar dabba, ya zauna cikin akuyoyi na tsawon lokaci da kokarin zama daya daga cikin su.

Hakan ya bashi damar zama daya daga cikin dabbobin, wanda basu iya banbance tsakanin kansu da shi ba, yanayi duk abu da sukeyi, baki daya rayuwar shi irin tasu yake yi. Hakan yasa basu gudun shi, sukan kusance shi kamar yadda suke kusantar ‘yayan su.

Binciken nashi dai ya bayyanar da abubuwa da dama, wanda hakan yasa aka bashi lambar yabo mai girma.