'Yan Kutse Na Biye Da Mutane A Ko'ina, Taya Za'a Iya Kare Kai?

Shugabar Kamfanin Yahoo Marissa Mayer.

Kimanin mutane sama da milliyan dari biyar 500, da kanyi amfani da asussun yanar gizo “Yahoo Account” wanda ‘yan kutse suka yima tabargaza. Wannan shine babban abu da ya taba faruwa da manyan kamfanoni a fadin duniya.

Duk dai da cewar an taba samun irin haka a shekarar 2013, wanda kimanin mutane milliyan dari uku 300, da ke amfani da assusun Myspace suka fuskanci irin wannan matsalar. Hukumomin kamfanin Yahoo sun daura alhakin hakan a kan jami’an gwamnati.

A cewar shugaban hukumar manyan laifuffuka ta FBI James Comey, tun a shekarar 2014, akwai wasu kamfanoni a kasar Amurka, da wasu kamfanoni a kasar China, ke yima kutse da kuma wasu kamfanoni da basu da ma masaniyar anayi musu irin wannan kutsen.

Kana ba’a ta’allaka wannan kutsen da kasar China, amma abun da yake so ya gaya ma mutane shine, su dinga daukar cewar a kowane lokaci, ana iya yimusu kutse don haka saisu dauki duk matakan da suka kamata don kare kansu.

Daraktan tsaro na kamfanin Yahoo, Mr. Dan Kamisky, ya kara jawo hankalin mutane a duk fadin duniya, da su kokarta wajen kare kansu, da kokarin canza password din su akai-akai, kana da gujema bude wasu sakonni da akan aika idan basu san sunan mai aiko da sakon ba.