Babu Nakassashe Sai Kassashe! Kowa Da Irin Baiwar Da Allah Yayi Mishi!

Mace Mai Zane da Kafafu.

Mace Mai Zane da Kafafu.

Allah mai baiwa da daukaka, ga duk wanda yaso a rayuwa. Babu dan’adam da Allah, ya halitta a duniya da bai masa irin nashi baiwar ba! Wata mata da bata dauki baiwar da Allah, yayi mataba a matsayin nakasa.

Swapna Augustine, mai shekaru arba’in 40, da haihuwa ‘yar kasar India, ta lashe tutar masu baiwar zane, duk dai da cewar bata da hannaye, amma zanen da takeyi da kafafuwan ta, sun kaita ga shiga cikin kundin tarihin duniya.

Ta kanyi zane da mutanen kauyen su kanyi mamaki, ta fuskanci matsaloli a rayuwa tun tana matashiyar ta, wanda ta kanyima kanta komai a rayuwa, ta kasance mace mai sha’awar zane, wanda takanyi amfani da damar da take dashi, na amfani da kafa wajen zanen abubuwa a rayuwar yau da kullun.

Takan yi amfani da ire-iren zane da ta gabatar a makarantu, ko mujalloli, don bama matasa kwarin gwiwa, ganin cewar idan ita da take da nakasa tayi wani abu, to inaga masu hannu, suma suna iya nuna nasu gwanintar a kowane bangare.

Batare da tunanin wani abu ba, a rayuwa yau gashi abun da ta dauka bashi da muhimanci, ya kaita ga zama wani abu, tana ganin idan mutun zai riki irin abun da yake da shi a tare da shi, to zai iya fice a duniya.