Kusan za’a iya cewa Mr. Brandon Paulin, shine shugaban karamar hukuma mafi karancin shekaru a fadin duniya. Kimanin shekara daya kenan data wuce, aka zabi Mr. Paulin, a matsayin shugaban karamar hukumar Indian Head, wata karamar hukuma a jihar Maryland ta kasar Amurka.
A dai-dai shekarar da ya kammala karatun shi na matakin sakandire, yana mai shekaru goma sha takwas 18, aka zabe shi yazama zababben shugaban karamar hukumar. Matashin dai yana shugabantar yawan mutane sama da dubu hudu, wadanda akwai tsofaffi masu shekaru da dama a cikin su, amma abun ban sha’awa duk wanda aka tambaya dangane da shugabancin shi, sai dai suce Allah san barka.
Ya bayyanar da kan shi a matsayin yaro mai son ganin ya taimaka ma wasu, tun yana dan yaron shi, kuma ya samu sha’awar son shugabancin karamar hukumar su, tun yana dan makarantar firamari, ya gayama iyayen shi lallai sai yayi shugaban karamar hukumar. Tun bayan shigar shi ofis, ya dau alwashin kawo kasuwanci da samar da hanyoyin kudin shiga ga karamar hukumar tashi.
Bayan shekara daya, ya bayyanar da irin cigaban da aka samu a karamar hukumar tashi, karkashin jagorancin shi. Yayi amfani da yaruntar shi wajen jawo kamfanoni da ‘yan kasuwa don su zuba jari a karamar hukumar ta su, wanda hakan yayi nasara. Bai kuma dogara da kanshi kadai ba wajen gudanar da aiki, yakan nemi shawara daga wajen magabata, da suke da sanin rayuwa fiye da shi.
An dai bayyanar da Mr. Paulin, a matsayin matashi da yakamata ace kowane matsahi yayi koyi da irin zuciyar shi, da irin kokarin ganin ya bada tashi gudunmawa a wajen cigaban al’umar shi a ko ina a fadin duniya.