Kamfanin Samsung Zai Fara Mayarwa Jama'a Sabuwar Wayar Samsung Galaxy Note 7, Da Ya Yi Kiranye

A kwanakin da suka gabata ne kamfanin wayar hannu wadda aka fi sani da Samsun, yayi kiranyen sabuwar wayar hannun da kanfanin ya fitar ba da dadewa ba wadda ya sawa suna Samsun Galaxy Note 7, har guda miliyan biyu da dubu dari biyar.

Kamfanin zai sake wa masu wayoyin wasu sababbin wayoyi ne a sakamakon rahotannin fashewar da batirorin wayoyi kirar Samsung Galaxy Note 7, guda 35 suka yi.

Dan haka idan kana da irin wannan waya, garzaya ka mayar da ita, ka amshi wata sabuwa a kyauta domin kaucewa irin illar da fashewar batirin wannan waya kan yi.

Wani sabon bincike ya bayyana cewa akwai hanyoyin da mai amfani da wayar Samsung Galaxy Note 7, ka iya gane alamun fashewar batirin na wayoyin su, amma sai dai kamfanin ya bada shawarar mayar da wayoyin domin karbar sababbi.