Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na Gaji Da Tukin Mota, Sai Na Kera Jirgin Sama!


Jirgin Sama
Jirgin Sama

Akwai gajiya yau da kullun, ace mutun yana tukin mota na wasu mintoci kamin ya kai wajen aiki. Hakan yasa Mr. Frantisek Hadrava, daga kauyen Zdikov, a kasar “Czech Republic” ya fito da wata sabuwar dubara.

Mr. Hadrava, ya kwashe tsawon shekaru biyu, yana kera jirgi mai tashi sama, wanda yace, madadin ya dinga tuki, da wani lokaci kamin zuwa wajen aiki, ya yanke shawarar ya kera wannan jirgin, wanda yake daukar shi mintoci bakwai ya isa wajen aiki.

Shi dai jirgin yana sauka a kan titin da motoci ke yawo akai, kana ya kanyi amfani da karfin shi wajen gyarama jirgin zama, bayan isa wajen aiki. Wannan ba karamar hikima bace gare shi, da yunkurin shi na rage yawan cunkoson motoci a kan hanya.

Sunan da ya sama jirgin shine “Vampira” wanda ya kanyi tafiyar kimanin kilomita dari da saba’in da biyar a tashi daya. Yana kuma shan galan daya na fetur a cikin awa daya. Baki daya kudin da ya kashe wajen hada jirgin, basu wuce kimanin dallar Amurka $4,150 dai-dai da naira milliyan daya da dubu dari bakwai.

Ya bayyanar da sha’awar shi da jirgi tun yana dan shekaru goma, da ya kalli wani fim na yakin duniya na biyu, tun lokacin yake da tunanin sai ya kirkiri nashi jirgin a rayuwa, wanda burin shi ya cika.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG