WASHINGTON D.C —
An yi bukin cikar gandun shakatawa na kasar Amurka shekaru 100 da kafuwa, wanda ke nan birinin Washington DC.
An gudanar da bukin ne a wajen da mutane suka fi ziyarta, gandu mai tsawon kilomita uku dake tsakanin ginin Majalisar Amurka da kuma gidan tarihi na Lincoln Memorial, wanda ke samun maziyarta kusan Miliyan 24 a duk shekara. A kusan tsakiyarsa akwai gini mai tsawo da ake kira Washington Monument.
Bikin na jiya Alhamis dai ya hada da abubuwa daban daban ciki harda wani bangare da ake nuna bayanan mata da mazan da sukayi aiki a gandun dajin, sai kuma guraren wasanni da na wasan yara.
An gudanar da bukin rantsar da sabbin ‘yan ‘kasa a gidan tarihi na tunawa da yakin duniya na biyu.