Jagorar tawagar ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya, a gasar wasanni na Rio Olympics 2016, John Mikel Obi, ya rubuta gajeruwar kasida, dangane da nasarar su a wasan da aka kammala.
A cikin kasidar, ya bayyanar da jin dadin shi da godiya ga sauran abokan wasanshi, haka da hukumomi da suka taimaka wajen samun nasarar. Bayan haka sai ya kara da cewar, a zahirin gaskiya idan ya duba wannan nasarar da sukayi, wata abun dubawa ce.
Domin kuwa tun a lokacin da yayi shirin barin klob din shi, na Chelsea, don ya buga ma kasar shi wasa, yayi tunanin cewar lallai wannan aiki ne ja, wanda idan ba suyi kamar sunayi ba, to babu shakka sunan kasar tasu zai iya shiga cikin wani hali.
Hakan ya kara sa shi tunanin taya zasu fitoma wasan don samun nasara. Wanda sunyi rawar gani baki dayan su, gwabzawar da su kayi da ‘yan wasan kasar Honduras, inda aka tashi da ci 3-2 itace ta basu nasarar samun Azurfa. Idan kuma akayi la’akari da kasar Najeriya bata sake samun wata lamba mai girma ba tun daga shekarar 2008.
Yayi godiya matuka ga abokan wasan shi, wanda yake cewar yanzu haka ya koma klob din shi, don cigaba da fuskantar wasu kalubale da suke gaban shi. Yayi godiya ta musamman ga masoya, da kuma karama matasa karfin gwiwa, da su dage da nacewa wajen atisaye da duk wasu abubuwa da kan iya kaisu ga nasara a rayuwa.