Kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil ta samu nasarar lashe lambar zinare a gasar Olympic da akayi a kasar ta Brazil mai take Rio 2016.
Brazil ta samu nasara ne akan takwararta kasar Jamus inda suka shafe mintina 90 suna fafatawa har aka tashi 1-1
Dan wasan Brazil Neymar shine ya jefa kwallon a ragar Jamani cikin minti 26 da fara wasan.
Ita kuwa kasar Jamus ta rama kwallon tane ta hanun dan wasanta mai suna Meyer a minti 59 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, daga bisani aka kara musu minti 30 amman haka aka tashi 1-1, sai da aka je bugun daga kai sai mai tsaron gida wato fenareti Inda aka tashi 5-4.
Wannan nasara da Brazil ta samu it ace ta farko a gasar ta Olympic da kasar ta taba cin lambar zinare a bangaren kwallon kafa amma ba shine zuwa wasanta na karshe a gasar ta Olympic ba.
Brazil ta taba zuwa final sau 4 a shekara ta 1984-1988-2012 sai kuma wannan shekara ta 2016 wanda ta samu nasara.
A tarihin karawar Brazil da Jamani kuwa an fafata sau 23, Brazil tayi nasara akan Jamani sau 13, ita kuwa jamani sau 5, ta taba samun nasara a kan Brazil, kuma sun yi kunnen doki sau 5.
Sai dai a karawarsu a baya kafin wannan Jamani ta lallasa Kasar Brazil daci 7-1 agasar cin kofin duniya da akayi na shekara 2014.