Wani Matashi Ya Yanka Cikin Budurwar Shi Saboda Ta ki Zubar Da Ciki

Wani matashi dan wata jami’a, a kudu maso yammacin Najeriya, mai suna Ade, yanzu haka yana hannun hukumar.

Shi dai Ade ana zargin sa da yankar budurwarsa da wuka a ciki wai domin ta ce it aba zata zubar da cikin da yayi mata ba.

Ade, ya aikata wannan ta’asar ne a gidan budurwar tasa dark unguwar Zango Alaro, dake garin Ibadan.

Su dai wadannan matasa sun sadu ne ta shafi sada zumunta ta facebook kimani watanin biyu da suka wuce, a ranar 10, ga wannan watan da muke ciki shine budurwar tashi ta ce masa tayi ciki shi kuwa ya bukace ta da ta cirea binda iyayen ta suka ce basu amince ba.

Shi kuwa Ade. a cewarsa baya son iyayen sa su san abinda ya faru sai yace ya shiga yanar gizo yana neman dabaru iri iri ta yadda zai bullowa al’amarin sai ya yake shawarar ya kashe ta saboda ita kadai ta san gidansu. Idan har ya kashe ta babu yarda iyayensa zasu sani.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Oyo, SP Adekunle Ajisebutu, wanda ya tabbatar da labarin yace za’a gurfanar da Ade a gaban kotu da zarar an kammal bincike, ita kuwa budurwarsa tana asibiti rai kwakwai mutu kwakwai.