RIO 2016: 'Yar-Tseren Mata, Ta Samu Nasara Da Barin Baya Da Kura!

'Yar tseren gasar Rio Olympics

A cikin jerin ‘yan tseren mata na wasan Rio Olympics, Shaunae Miller, ‘yar kasar Bahamas, ta kafa tarihi da bada mamaki, a yayin tseren su na mitoci dari hudu, ta kawo karshe amma bata iya saka kafaffuwan ta don tsallake layin karshe ba.

Amma abun da tayi shine, sai ta kwanta don mika hannun ta da ya tabbatar mata da wannan nasarar, ta zamowa mace da ta lashe kyautar Zinariya. Jim kadan bayan an sanar da cewar ita ta lashe gasar, sai ta bayyanar da cewar.

“Ban taba yin haka ba, duk dai da cewar nasamu raunuka, a dai-dai lokacin da na fadi don zama zaka, amma babu komai nasarar ta biya” Tace a gaskiya lokacin da na fadi, ban taba tsammanin cewar na lashe gasar ba. Sai da aka sanar, kuma nayi mamaki matuka.

‘Yar wasan tseren mai shekaru ashirin da biyu 22, ta lashe wannan kambu ne, a cikin mintoci arba’in da tara da dakika arba’in da hudu 49.44. Wannan nasarar da ta samu ta kawo rudani da yawa, don ba’a taba samun irin hakan ba.