Akwai Babban Barazana Da Matasa Suke Fuskanta

Abdulmajid Babangida Sa'ad

Shugaban wata kungiya mai rajin samarda zaman lafiya a nahiyar Afirka Abdulmajid Babangida Sa’ad, ya ce kungiyar su da hadin kan wasu kungiyoyi a gida da waje na gudanar da aiki tukuru don samawa matasa hanyoyin dogaro da kai.

Yana mai cewa akwai babban barazana da matasa suke fuskanta, domin a yanzu a tsare tsaren da ake yin a gwamnatoci a matakai daban daban ba’a tuntubarsu wajan zana manufofin da tsare tsaren gwamnati ta hanyar da zai taimaki rayuwarsa, hakan yasa matashi ya shiga tsaka mai wuya.

Babangida Sa’ad, ya kara da cewa a kungiyance basu samun damar iya gudanar abubuwan da suke da muradi a ko0wane lokaci sai dai a wasu lokuta suka hada guiwa da wasu masu ruwa da tsaki, masamman wadada suke samun tallafi da wasu kungiyoyi na duniya.

Kamar yadda masu ruwa da tsaki ke bayanin cewa halin da matasa suka sami kan su a cikina kara tabarbarewa, inda suke kira ga hukumomi da su gaggauta kawo wa matasa dauki kafin matsalar ta gagari kundila.