Kamfanin shafin zumunta na facebook, sun fitar da wata sanarwar garon bawul, da sukayi ma shafin su. Wanda yake nuni da cewar mutane masu son gulmar abubuwa da suke faruwa, da shahararrun mutane ko siyasar duniya, sai su kara gyara zama, domin sun fito da wata sabuwa garabasa.
A cewar kamfanin, yanzu madadin mutane su dinga samun sako, da yake nuna musu cewar an saka wani labari da ya kamata su karanta, amma ba zai basu takaitaccen labarin ba, sai dai ya nuna musu alama kawai, "clickbait."
Wanda hakan yasa wasu mutane da dama nuna rashin jin dadin su, hakan yasa kamfanin sake tsarin, yanzu haka dai idan akwai wani labari ko gulma dake faruwa, da wasu mutane kodai ‘yan fina-finai, ko ‘yan kwallo, ‘yan siyasa, da dai makamantan su, labari zai dinga shigowa cikin wayar su, da takaitaccen bayanin abun da labarin ya kunsa.
Hakan zai ba mutane damar sanin meke kunshe a cikin labarin, idan suna da bukatar karantawa sai su karanta, idan kuma basu da bukata sai su cigaba da harkokin gaban su, wannan zai magance matsaloli da dama, wajen tattalin sinadarin shiga yanar gizo “data”