Mai gwagwarmayar rajin kare hakkin bil Adama a Indiya, Irom Sharmila, ta kawo karshe yajin cin abincin da ta kwashe shekaru 16 tanayi, ta kuma sha alwashin ci gaba da fafutukar ganin an samar da doka da zata baiwa sojoji damar shiga harkar siyasa.
A jiya Talata ne Sharmila ta bude bakinta gaban manema labarai, inda ta lashi zuma daga hannunta, ta kuma ce “ba zan taba mantawa da wannan lokacin ba.”
Safiyar jiya Talata ne wani Alkali ya bayar da belin Sharmila, bayan da ta amince da cewa zata dawo da cin abincin ta.
An kwantar da Sharmila a Asibiti, inda anan ne ma aka saka mata bututun roba a hancinta domin ciyar da ita ta dole, bayan da ta fara yajin aikin cin abinci a watan Nuwambar shekara ta 2000.
Tace ta na shirin yin takara a zabe mai zuwa a kauyen da ta fito dake Arewa maso Gabashin jihar Manipur.
Sharmila dai ta fara yajin ‘kin cin abinci ne bayan da aka baiwa jami’an tsaron kasar garkuwa karkashin wata doka, inda har suka kashe wasu mutane 10 ba tare da an bincikesu ba, haka kuma gwamnatin kasar ta ci gaba da cin zarafin mutanen da basa goyon bayanta.
An dai tuhumeta da laifin kokarin kasahe kanta, wanda yake laifi ne a kasar Indiya.
Ta yanke shawarar kawo karshen yajin cin abincin ne domin kawo karshen zanga zangar da akeyi, yayinda gwamnati ta nemi jami’an tsaron kasar da suyi amfani da damar da doka ta basu don kawo karshen zanga zangar da ta barke a yankin Kashmir. Dokar dai ta baiwa jami’an tsaro damar tsare ko kuma kashe duk wani ‘dan aware ba tare da tsoron gurfana a gaban shari’a ba.