RIO: Kasar Kenya Ta Dakatar Da Shugaban Tawagar 'Yan Wasan Su!

Rwanda Rio 2016

A dai-dai lokacin da ake kigaba da gudanar da wasannin Rio Olympics, a kasar Brazil, sai ga wani rahoto da yake bayyanar da cewar, shahararren dan tseren kasar Kenya, dake jan ragamar ‘yan wasan kasar. Ya bayyanar da cewar zai kare duk wani dan wasa daga gwajin da za’ayi musu don tabbatar da cewar basu sha wata kwaya ba.

A tabakin sakataren wasanni na kasar Kenya, Mr. Hassan Wario, ya jaddada cewar za’a maida shugaban ‘yan wasan gida Kenya, kuma za’a hannunta shi ga hukumomi don gudanar da bincike akan wannan zargi. Kuma idan aka same shi da wannan laifin babu abun da zai sa ba za’a hukunta shi yadda ya kamata ba.

A cewar jaridar Time newspaper ta kasar Ingila, an sami wani bidiyo da ake gabatar da cinikayya da Mr. Rotich, da cewar zai kare su idan za’a biya shi kimanin dalar Amurka, dubu goma sha uku $13,000. Wanda zai kokarta wajen ganin ya shashantar da sakamakon gwajin. Wanda hakan zai ba ‘yan wasan damar cin nasarar gasar, domin kuwa ba zasu gaji ba a lokacin da suke gudanar da wasan.