Ya Yiwa 'Yar Shekaru Bakwai Fyade

.

An gurfanar da wani matashi mai suna Modiu Diallo, a gaban wata kotu, dake Suru-Lere a jihar Legas, wanda ake Zargi da yiwa wata yariya 'yar shekaru bakwai fyade.

Sgt. Anthonia Osayande, wacce ta gabatar da kara a madadin 'yan Sanda ta ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 13, ga watan Yuli, da misalin karfe 6, na safe a harabar babban Masallacin Iponri a Suru-Lere.

Ta kara da cewa laifin ya sabawa sashe na 135 da Kuma sashe na 137, na kundin dokar jihar Legas, na shekarar 2011.

Alkalin kotu mai shara'a Ekpaye Nwachuku, ta badea belin wanda ake zargin akan kudi Naira dubu 500,kuma ta daukaka karar zuwa 20, ga watan Satumba.