A yau mun sami zantawa da wata matashiya mai suna Maimuna wacce ta bayyana wasu matsalolin da da suke fuskanta kafin kammala karatun digiri.
Malama Maimuna wacce ta ce tun daga lokacin karbar takardan daukarta karatu ta fara fuskanta kalubale, kama da kwasakwasan da ta ke yi wanda ta shafe adadin shekaraun da ya kamata ace mutun ya kammala karatun.
Ta kara da cewa rashin kyawawan tsarin na adana aiyukan da dalibai suka yi wanda a wasu lokuta akan nemesu a rasa saboda babu adani mai kyau.
Ta kuma bukaci matasa maza da mata da a nemi ilimi kuma a koyi sana’a domin ba lalle ba ne duk a samu aiki gwamnati, saboda haka koyon sana’a ya zama wajibi.