Watanni Biyar Babu Albashi Daga Hukumar NFF In Ji Siasia

Samson Siasia

Mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru ashirin da ukku U-23, Samson Siasia, yace watani biyar kennan hukumar kwallon kafa ta Najeriya, bata biyashi albashi ba.

Siasia dai yanzu yana Atlanta, tare da ‘yan wasan Flying Eagles, inda suke ci gaba da shirye shirye dagane da wasani Olympic da za’a gudanar Rio, ta kasar Brazil.

Siasia, ya ce suna cikin mawuyacin hali, yana mai cewa tun da suka sauka Amurka domin horar da ‘yan wasan ba wanda ya aiko masuda kudi.

Ya kara da cewa baza suyiwa Najeriya yankar baya ba amma yakamata gwamnatin Najeriya ta kawo mana dauki.

Ana sa ran cewa ;yan wasan zasu tashi ziuwa Brazil ranar juma’a