Daya Daga Cikin Kunkurai Uku Ya Tafi Yawon Ganin Gari Ne-Inji Mai Shi

Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Amurka a birnin New York sun sake gama wani mutum da dan kunkurunsa da suka tsinta yayin da suka ganshi a gefen hanya yana ta tafiya.

A cewar mai Magana da yawun jami’an ‘yan sandan, direban wata babbar motar Bus data ajiye jama’a ne ya ja hanaklin su akan kunkurun, wanda ya yi nisa akan hanyar sa ta barin birnin zuwa makwabciyar jihar.

Yayin da jami’an ke rike da wannan kunkuru a ofishinsu har kusan tsawon sa’a guda, wani mutum ya shiga ofishin rike da wani kunkurun inda ya bayyana masu cewa kunkurun sa ne.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya bayyana ma jami’an cewa barci ne ya kwashe shi dalilin daya sa kunkurun ya bar sauran abokansa guda biyu cikin jakar da mutumin yake dauke da ita, ya kuma kara da cewa bayan ya farka daga barci ne yaga cewa guda ya fita kuma kafin ya gano shi sauran guda biyun da suka rage ma sun tafi yawon ganin gari amma ya gano su.