Zainab Indomie Da Ali Nuhu Na Aiki Akan Wani Sabon Fim

Jarumin Fina-Finan Hausa, Ali Nuhu

Hazikar jaruma Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie da aka kwashe watanni barkate batare da jin, duriyarta ba ko kuma ta fito a fina finai a jiya Talata ta fara aikin wani babban shiri da aka yi wa lakabi da JINSI na kamfanin MIS Poduction, Jos da ke jahar Filato.

Jarumar dai a yanzu haka na can garin Jos fagen daukar fim din JINSI wanda uban gidanta Ali Nuhu ya shirya kuma fitaccen daraktan nan da ya fito daga garin Jos Yusuf Khalid ke bada umarni.

A yanzu haka ana sa ido a ga irin rawar da Zainab zata taka a wannan sabon fim ganin cewa an kwashe tsawon lokaci batare da fitowa a fim ba.