Hukumar kwallon kafa ta duniya watau FIFA, tace zata kara kasashe takwas a gasar cin kofin kwallo ta duniya a shekara ta 2026, inda zai zamo jimilar kasashe arba’in kennen zasu fafata a gasar.
Shugaban hukumar Gianni Infantino, ne ya bayan haka a lokacin ziyarar daya kawo Najeriya.
Shugaban ya ce Karin kasashen takwas da za’a yi a gasar cin kofin duniya, hukumar FIFA, tayi alkawarin zata bada Karin kasashe biyu wa yankin nahiyar Afirka, a yanzu haka kasashe biyar ne ke wakiltar nahiyar ta Afirka.
Shugaban na FIFA, ya bayanawa hukumar kwallon ta Najeriya NFF, cewa Najeriya zata sami Karin kaso na kudin da FIFA, take baiwa Najeriya daga dala dubu dari biyu zuwa dala miliyan daya da dubu ashirin da biyar kimani Naira Biliyan ukku da dubu dari tara .
Your browser doesn’t support HTML5