Malama Juwairiya Abdulmalik daliba mai koyan makaman aiki a asbitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta ce yajin aikin da jami'oi, ke yi a gida Nijeriya ne ya sa ta fita kasar waje domin yin karatunta na digiri, a waje domin karatun da mutun zai yi a cikin shekaru hudu wasu lokuta sai an wuce shekaru biyar kafin dalibai su kammala karatun saboda yajin aikin Malaman jami’oi.
Ta kara da cewa yadda ake tafiyar da koyarwa a waje yafi na gida Najeriya masamman wajan kayayyakin koyarwa na zamani da kuma irin ma’amala ta mai koyarwa da mai koyo.
Ko da yake duk da fita wajen da tayi domin neman ilimi hakan na tattare dawasu kalubale na rayuwa, domin kuwa a cewarta ko da ta tafi Dubai domin neman ilimi ta fukanci matsalolin wariyar launin fata da tsangwama daga wasu dalibai har ma da wasu daga cikin malaman da suka koyar da ita a I jami’a.
Juwairiya ta kara da cewar haka ya taimaka mata wajen gogayya da wasu dalibai daga wasu kasashen duniya , inda take cewa burinta ta kammala koyan aikin ta fara aiki a kasarta ta Nijeriya daga bisani ta karo ilimi a digirinta na biyu amma fa a nan gida Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5