Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wsan Kwallon Kafa Na Duniya

Kingiyar kwallon kafa ta chelsea tasa zunzurutun kudi har fan miliyan £62, domin sayen danwasan Real Madrid mai suna Alvaro Morata.

Sai dai mai horas da Kungiyar ta Real Zinedine Zidane, yace bazata sabu ba domin yana so Morata, ya zamo daya daga cikin ‘yan wasa 11 da zai fara wasa da su a kakar wasan Laliga ta bana 2015/2016.

Man City na dab da sayen dan wasan Schalke 04, mai suna Leroy Sane, dan shekaru 20 da haihuwa akan kudi fan miliyan £42, Yayin da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ke neman dan wasan Inter Milan mai suna Mauro Icardi, akan kudi fan miliyan £40.

Ita kuwa Kungiyar Real Madrid dake kasar Spain ta ce bata bukatar dan wasan gaba na Kungiyar Bayern Munich a yanzu mai suna Robert Lewandoski

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na zawarcin dan wasan Barcelona mai suna Arda Turan, dan shekaru 29 da haihuwa.