An Kama Wata Motar Fataucin Yara

Hukumar shige da fice ta Najeriya, reshen jihar Ebonyi, ta kama wata motar haya dauke da mutane har da yara wadanda ake zargin cewa anyi fataucin su ne.

An kama motar ne akan hanyar ta na zuwa jihar Edo, daga garin Bekwara a jihar Cross River.

Mukaddashin shugaban hukumar shige da fice na jihar ta Ebonyi, Barrister Okey Ezugwu, wanda ya tabbatar da labarin ga manema labarai a Abakaliki, ya ce motar da aka kama su da ita mallakar gwamnatin jihar Ondo ne.

Ya ce yaran sun ce za'a kai su jihar Ondo ne inda wasu kuma suka ce za'a kai su aikin ne a gonar Koko. jami'in ya kuma gargadi iyaye dasu guji dabi’ar baiwa mutane ‘ya’yan su saboda kudi ko kuma na wani biyan bukatar su.