Dukan Wani Matashi Zai Sa A Kori 'Yan Sanda

‘Yan sanda

Wani matashi dan shekaru 28, ya zargi ‘yan sanda jihar Akwa Ibom, da asabtar dashi da kuma yi masa sata.

Shi dai wannan matashi mai suna Ndifreke Ibuotenang, ya ce ‘yan Sandan gundumar Mkpat Enin, a dake jihar ta Akwai Ibom, sun nakada masa duka.

A cewarsa wannan ya faru ne da misalign karfe 9, na dare akan hanyarsa na zuwa gida daga wurin shan bammi.

Da aka tuntubi Kwamishinan ‘yan Sandan jihar, Murtala Mani, ya ce tuni hukumar ‘yan Sanda ta fara bincike akan lamarin, kuma ‘yan Sandan da ake zargin suna tsare.

Ya kara da cewa idan har zargin ya tabbata za’a gurfanar dasu a kotu kuma zai kasance sanadiyar rabuwarsu da aikin dan Sanda.