Matasa Da Dama Sun Halarci Taron Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Taron yaki da cin hanci da rashawa ya sami halartar matasa maza da mata da ‘yan makaranta, kungiyar yaki da cinhanci da wanzar da zaman lafiya ce ta shirya wannan taro a birnin Abuja.

Gayyatar matasan ta nuna zummar cusawa manyan goben akidar kumar cin hanci da rashawa tun basu fara ayyukan gwamnati ko rike wasu mukamai ba.

Injiniya Zakari Ahmad Guroje shine shugaban kungiyar kuma ya bayyana cewa jama’a sun mayar da yaki da cin hanci da rashawa tamkar abinda ya shafi shugaban kasa ne kawai, dan haka ba daidai bane, wannan yaki ne daya shafi kowa da kowa domin kuwa duk wani dan Najeriya yasan cewa cin hanci da rashawa babbar annoba ce a wannan kasa.

Shugaban ya cigaba da cewa kowa na bukatar sa hannu domin ganin an sami mafita daga cikin wannan kangi da kasar ta sami kanta.

Babban mai taimakawa shugaban Najeriya na musamman akan harkokin siyasa Gideon Sammani yace gwamnatin Buhari bazata saukakawa barayin biro ba, ya kuma kara da cewa idan kaduba EFCC suna aiki, ICPC haka kuma SSS, da masu shari’a a kasar duk suna aiki, dan haka dole ne a hada hannu domin a yaki wannan shedan, wato cin hanci da rashawa.

Bako mai jawabi masanin harkokin siyasa dr Sadiq Abba yace korafin kuncin talauci da ‘yan Najeriya ke yi ba dai dai bane, domin nasa ganin dole ne duk kasar data sami cigaba, to lallai ne sai ta fuskanci kunci kafin daga baya jin dadi ya biyo baya.

Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Da Dama Sun Halarci Taron Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa