Ya Yiwa 'Yar Shekaru 10 Fyade

REUTERS/Mariana Bazo (PERU - Tags: CRIME LAW DRUGS SOCIETY) - RTX12OBY

Kungiyar ‘yan jarida mata reshen jihar Cross Rivers, da hadin guiwar kungiyar Lauyoyi mata ta duniya domin tabbatar da ganin cewa wani mutun mai suna Malam Bashir, wanda ake zargi da lalata wata yariya ‘yar shekaru 10, da haihuwa bai sami beli ba.

Ita dai wannan yarinyar da aka tafkawa wannan aika aika tuni Allah yayi mata rasuwa sanadiyar tursasamata da akayi .

Shugabar kungiyar mata ‘yan Jarida Ms. Lillian Okonkwo, tace ‘yan uwa da abokan wanda ake zargin suna kokarin ganin cewa an bada belin sa.

Ta kara da cewa abin takaici ne abinda ya faru gashi kuma yarinyar mata ta mutu, amma a cewar ta sun kira ga hukumomi cewar kada a bada belin wanda ake zargin.