Daliban Kwalejin Ilimi Sun Yi Zanga Zanga

Hukumar kwalejin ilimi na Gwamnatin tarayya na Alvan Ikoku, dake Owerri, cikin jihar Imo, ta bayana rufe makarantar har sai ila masha Allahu.

Rufe makarantar ya biyo bayan wani zangazanga da daliban suka yi a yau litinin, kamar yadda shugaban makarantar Dr. Blessing Ijeoma, ta tabbatar.

Ta kara da cewa hukumar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan barnar da daliban suka tafka wanda suka hada da yin kacha kacha da ginin gudarnarwa na makarantar da lalata motocin gwamnati guda tara.

Daliban suka ce zanga zangar ya biyo bayan Karin wasu kudade da hukumar kwalejin tayi da suka hada da kudin rajistar farko daga Naira 10,000 zuwa Naira 30,000. Da kuma kudin makaranta daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000.

Shugaban makarantar tace daliban basu da wata hujjar yin zanga zangar, zauna gari banza sun yi amfani da wannan damar wajen sace sace wanda suak hada da kwamfutocin makarantar.