Dan wasan gaba na kungiyar wasan kwallon kafa na Juventus, Paul Pogba, yace tana iya yuwa ya koma kungiyar Manchester United, a nan gaba.
Ana rade raden cewa Pogba, zai bari Italy, a bazarar wanna shekarar kuma Real Madrid da Manchester United, duk suna zawarchi sa da ya rattabamasu hannu domin ya buga masu ta maula.
Pogba wanda ya bar Manchester United a shekarar 2012, yanzu haka ana neman fam din Igila miliyan100, akansa.
Da aka mika masa jersey na kungiyoyin ukku sai yace “ Juventus kungiya tace iyalai na ne kuma ita nake yiwa wasa idan na saka jersey ta ina farin cikin buga tamaula, abinda nake da muradi ne tun ina dan yaro."
Da aka mika masa na Manchester United sai yace dasu na fara iyalai nan a farko kennan, ita kuwa kungiyar Real Madrid, cewa yayi gawurtatciyar kungiyar ce.